Isa ga babban shafi
Nijar

Yan Boko Haram sun kaiwa sojojin Nijar Hari a Jihar Diffa

Wasu da ake zargin cewa magoya bayan kungiyar Boko Haram ne, sun kashe jami’an tsaron jamhuriyar Nijar 6 tare da raunata wasu uku a wani wuri mai tazarar kilomita 20 daga garin Diffa.

Wasu sojojin da yan kungiyar Boko Haram suka kashe
Wasu sojojin da yan kungiyar Boko Haram suka kashe
Talla

Sanarwar da ma’aikatar cikin gidan kasar ta fitar ta ce ‘yan Boko Haram sun yi wa sojojin kwanton bauna ne a lokacin da suke sintiri a yankin na Diffa dake kusa da iyaka da tarayyar Najeriya.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar na kokarin gani ta kawo karshen ta’adanci a yankin Diffa dake iyaka da kasashen Cadi da Najeriya a cewar ma’aikatar cikin gidan Jamhuriyar Nijar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.