Isa ga babban shafi
Liberia

Alkalan Liberia na ci gaba da tattaunawa dangane da batun zabe zagaye na biyu

Al’umar kasar Liberia na dakon hukuncin da Kotun Koli dake kasar za ta zartas gameda korafin da aka gabatar mata dake cewa hukumar zaben kasar ba ta shirya ba domin zagaye na biyu na Babban zaben da aka shirya gudanarwa ranar Talata 7 ga wannan  watan.

Kotun kolin kasar Liberia
Kotun kolin kasar Liberia Supreme Court of Liberia
Talla

‘Yan adawan kasar ne suka gabatar da korafin nasu gaban kotun, suna zargin hukumar zaben kasar, inda har suke neman a sauya manyan jamian hukumar, saboda takaddamar da aka samu.

Charles Brumskine ya kasance shine na uku a zaben zagaye na farko da aka gudanar ranar 10 ga watan jiya, kuma ya kalubalanci sakamakon zaben da cewa an yi magudi.

A wannan mako ne dai ya shigar da kara gaban kotun al’amarin da ya sa ake tababan zaben zagaye na biyu tsakanin shahararren dan kwallon kafa George Weah da kuma mataimakin shugaban kasar mai barin gado Joseph Bokai.

Hukumar zaben ta bukaci a shiga zagaye na biyu ne saboda babu dan takaran da ya samu kashi 50% na yawan  kuri’un da aka jefa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.