MDD ta kara dakarun wanzar da zaman lafiya a CAR
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da karin dakaru 900 domin karfafa rundunar wanzar da zaman lafiya da tsaro a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Wallafawa ranar:
Kara adadin dakarun wanzar da zaman lafiyar ta Minusca na daga cikin alkawurran da babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya dauka lokacin da ya ziyarci kasar a cikin watan jiya.
Har ila yau Kwamitin Tsaron ya amince da tsawaita wa’adin aikin rundunar da ke kokarin wanzar da tsaro da zaman lafiya a kasar mai fama da yakin basasa tun a shekara ta 2013.
Kafin wannan kari dai, akwai dakaru dubu 11 da 650 da suka hada da ‘yan sanda dubu biyu da 80 da ke aiki a karkashin rundunar ta Minusca, to sai dai ko baya ga gazawa ta fannin samar wa fararen hula tsaro, hatta su kansu dakarun na fuskantar hare-hare daga ‘yan bindiga.
Sai dai kara adadin dakarun na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta fara aiwatar da siyasarta ta rage kudaden da take kashewa domin tallafa wa ayyukan wanzar da zaman lafiya a sassan duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu