Isa ga babban shafi
Saliyo

Kotun kolin Saliyo ta dakatar da zaben makon gobe

Kotun kolin kasar Saliyo ta bada umurnin dakatar da shirin zaben shugaban kasar zagaye na biyu da aka shirya yi ranar talata mai zuwa, saboda korafin da Jam’iyyar APC ta shigar a gaban ta.

Julius Maada Biyo,na Jam'iyyar SLPP da ke shirin karawa da Samura Kamara a zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar da aka tsara gudanarwa a makon gobe.
Julius Maada Biyo,na Jam'iyyar SLPP da ke shirin karawa da Samura Kamara a zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar da aka tsara gudanarwa a makon gobe. REUTERS/Olivia Acland
Talla

Kotun ta umurci hukumar zaben kasar da ta jingine shirin gudanar da zaben zuwa ranar litini da zata yanke hukunci kan karar dake gaban ta.

Ana saran hukumar zaben ta gabatar da bayani kan zargin da ake mata, wanda kotun zata yi amfani da shi wajen yanke hukunci.

Julius Maada Biyo da Samura Kamara ne ake saran su fafata a zaben shugaban kasar zagaye na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.