Isa ga babban shafi

Buhari ya yi fatan alkhairi ga masu sauya shekar siyasa a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike da sakon fatan alkhairi ga Ilahirin ‘yan siyasar da suka sauya sheka daga wata jam’iyyar zuwa wata a dai dai lokacin da babban zaben kasar ke karatowa.

Muhammadu Buhari ya ce sauya shekar ta wasu daga mambobin Jam'iyya mai mulkin ba zai hana shi ci gaba da ayyukan raya kasa ba.
Muhammadu Buhari ya ce sauya shekar ta wasu daga mambobin Jam'iyya mai mulkin ba zai hana shi ci gaba da ayyukan raya kasa ba. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Muhammadu Buhari yayin wani taron cin abinci rana da ya gudana tsakaninsa da gwamnonin Jam’iyyar ta APC ya ce kowanne dan siyasa na da dalilin sauya sheka zuwa wata Jam’iyya.

A cewar shugaban na Najeriya, sauya shekar ta wasu jiga-jigan siyasa a kasar ba zai kawo tsaiko ga ayyukan da gwamnatinsa ke yi don gina kasar ba.

A baya-bayan nan ne dai wasu tarin jiga-jigan Jam’iyyar ta APC suka sauya sheka zuwa babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ciki kuwa har da shugaban Majalisar Dattijan kasar Bukola Saraki.

Sauran wadanda suka sauya shekar sun hada da Samuel Ortom Gwamnan Benue da Abdulfatah Ahmed Gwamnan Kwara da Godswill Akpabio tsohon Gwamnan Akwa Ibom.

Galibin dai masu sauya shekar sun nuna rashin amincewa da salon mulkin Muhammadu Buhari wanda ya karbi shugabancin a shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.