Isa ga babban shafi
Afrika

Afirka ce ta fi cutuwa da illar dumamar yanayi a duniya- masana

Babban Jami’in Diflomasiyar Masar da ke jagorantar kasashen Afrika a taron sauyin yanayi na COP25 da ke gudana a birnin Madrid na Spain, ya bayyana Afrika a matsayin yankin da matsalar dumamar yanayi ta fi yi wa illa, lura da ibtila’o’in guguwa da fari da kuma ambaliyar ruwa da suka tsananta a shekarun baya-bayan nan a nahiyar.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayin jawabinsa a taron wanda ke gudana a Spain.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayin jawabinsa a taron wanda ke gudana a Spain. REUTERS/Sergio Perez
Talla

Jami’in Diflomasiyar kuma mai rajin kare muhalli Mohammed Nasr ya bayyana haka ne a yayin wata zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP, inda ya ke cewa, Afrika nada muradun da ta ke fatan cimmawa, abin da ya sa ta shiga cikin yarjejeniyar sauyin yanayi da aka rattaba wa hannun a birnin Paris na Farasa.

Nasr ya bayyana fargabarsa kan rahoton kwararru na Majalisar Dinkin Duniya da ke nuna cewa, Afrika za ta yi dumi da kashi 2 a ma’aunin zafi, wanda kuma hakan ya zarce iyakar da aka saba gani.

Jam’in ya ce, akwai bukatar nazari kan wannan al’amari, yayin da ya yi shagube ga Amurka wadda ta janye daga yarjejeniyar birnin Paris duk da cewa tana gurbata duniya da akalla kashi 18.

A gefe guda, Nasr ya bayyana damuwa kan yadda kasashen Afrika da suka hada da Somalia da Ghana da Tanzania da Mozambique da Masar da Afrika ta Kudu ke fuskatar kalubale wajen habbakar tattalin arzikin al’umominsu saboda basukan da suka yi musu katutu da kuma yadda ake ninka musu kudin ruwa.

Kazalika jami’in ya alakanta talauci da jan-kafar da ake samu wajen magance sauyin yanayi a Afrika, inda ya bada misalin cewa, ba abu ne mai sauki ba a hana amfani da baburan a-daidaita-sahu masu fitar da gubataccen hayaki a kasashen Afrika domin kuwa babu wani tanadi da aka yi wa direbon da ke wannan sana’ar. .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.