Isa ga babban shafi
Afrika-Mauritius

Mauritius ta yi shelar kawar da annobar COVID-19

Gwamnatin Mauritius ta yi shelar samun nasarar kawo karshen annobar coronavirus ko COVID-19 a kasar, inda aka sallami dukkanin mutanen da a baya suka kamu da cutar, bayanda gwaji ya tabbatar cewa sun warke sarai.

Wani hoto da aka dauka daga jirgin sama, dake nuna yadda al'ummar kasar Mauritius ke bin doka ko ka'idar nesa-nesa da juna saboda coronavirus, yayinda suke dakon shiga kasuwa domin sayayya. Afrilu, 2020.
Wani hoto da aka dauka daga jirgin sama, dake nuna yadda al'ummar kasar Mauritius ke bin doka ko ka'idar nesa-nesa da juna saboda coronavirus, yayinda suke dakon shiga kasuwa domin sayayya. Afrilu, 2020. L'Express Maurice/AFP/File
Talla

Kawo yanzu dai an shefe kwanaki 17 ba tare da samun wani da ya kamu da cutar ta coronavirus a kasar ta Mauritius ba, a cewar ministan lafiyarta Kailesh Jagutpal.

Karo na farko kenan da wata kasa a nahiyar Afrika ta sanar da kawo karshen annobar COVID-19, cutar da yanzu haka ke cigaba da addabar sassan duniya musamman yankin Turai da Amurka.

Kasar Mauritius itace ta farko a nahiyar Afrika da ta soma kafa dokar kulle kuma mafi tsauri a ranar litinin 23 ga watan Maris, wadda a karkashinta sai da ilahirin kasuwanni da manyan shagunan saida kayayyaki suka shafe kwanaki akalla 10 ba tare da an bude su ba, matakin da gwamnatin kasar tace zai cigaba da wanzuwa zuwa ranar 1 ga watan Yuni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.