Isa ga babban shafi

Ambaliya ta ritsa da mutane a Afrika ta Kudu

Ambaliya ta yi sanadiyar mutuwar mutane 45 a Afrika ta kudu,an dai share kwanaki ana tafka ruwan sama daidai da baki kwariya.Hukumomin kasar sun aike da karin jami'ai don kai dauki ga jama'a da lamarin ya ritsa da su.

Ambaliyar ruwan sama
Ambaliyar ruwan sama http://www.youtube.com/screenshot RFI
Talla

Gwamnatin kasar ta aike da karin sojoji da nufin kai dauki ga mutanen da al’amarin ya ritsa da su,rahotanni daga yankin Durban na Kwazulu- Natal na nuni cewa jama’ar yankin na cikin wani mawuyacin hali.

Iftila'in ambaliya
Iftila'in ambaliya © AP

Akala gidaje sama da 2.000 ne suka rushe,yayinda wasu gidajen da aka gina ba bisa ka’ida ba 4.000 suka fadi kamar yada  hukumar magajin garin yankin ta sanar.

 

A gabar tekun birnin Durban,ana hango tarkace da dama da suka hada da robobi,karafe,ruwan sama sun janyo datsewar hasken wutar lantarki dama janyo datsewar ruwan sha a wasu yankuna ga baki daya.

Magajin birnin na Durban Mxolisi Kuanda ya sheidawa manema labarai cewa an samu asarar rayuka sanadiya wannan ambaliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.