Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Adadin wadanda ambaliyar ruwan Afrika ta Kudu ya kashe ya haura 306

Hukumomin Afirka da Kudu suka ce adadin wadanda suka mutu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a birnin Durban da ke kusa da tashar jiragen ruwa na kasar ya kai 306, bayan da shafe hanyoyi da tsaunuka, tare da lalata gidaje da gadoji.

Wata mujami'a da Amballiya ta rusta da ita a yankin KwaZulu-Natal dake Afirka ta Kudu.
Wata mujami'a da Amballiya ta rusta da ita a yankin KwaZulu-Natal dake Afirka ta Kudu. AP
Talla

Da farko babbar jami’ar kula da lafiya a yankin da aka samu iftila’in Nomangugu Simelane-Zulu ta tabbatar da adadin, inda take cewa ya zuwa daren Talata sun aje gawarwakin mutane 253 a asibitocin su guda biyu.

Jami’ar ta ce ya zuwa wannan lokaci suna cikin fargaba, domin dakin ajiye gawarwakin ya cika ya batse, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin ceto.

Ramaphosa

Shugaban kasa Cyril Ramaphosa wanda ya ziyarci yankunan da aka samu hadarin yace da sun saba ganin iftila’in na afkawa wasu kasashe irin su Mozambique da Zimbabwe, amma yau gashi suna gani a gida.

Mafi muni cikin shekaru 60

Rahotanni sun ce an kwashe shekaru 60 ba’a taba ganin irin ruwan saman da aka gani jiya ba, wanda ya rusa gidaje da gadoji da wanke hanyoyi da kada turaku da kuma tarwatsa kwantainoni a tashar jiragen ruwan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.