Wani farin fata ya bindige wata baka da ya dauka dorinar ruwa ce
‘Yan sanda a Afrika ta Kudu sun ce waani manomi farar fata ya harbe wata mata bakar fata da ya ce ya dauka dorinar ruwa ce.
Wallafawa ranar:
An dai kama mutumin Paul Hendrik van Zyl mai shekaru 77 a ranar Talata da ta gabata, bayan da yayi wannan harbin a kusurwar da matar take kamun kifi a wani kogi dake garin Lephalale a yankin arewacin Limpopo tare da abokiyar kamun kifin ta.
Mutumin na fuskantar tuhuma ce a kan yunkurin kisan kai a cewar masu gabatar da kara na kasar, duba da cewa raunuka matar ta samu.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Mamphasa Seabi ya ce lallai, ana tunanin wanda ake zargin ya harbi matar ce a lokacin yake zaton dorinar ruwa ce a wurin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu