Isa ga babban shafi

Kimanin mutane 341 ne suka mutu a Afrika ta kudu yayin ambaliya

Hukumomin Kasar Afirka ta Kudu sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliya da zaftarewar kasar ya kai 341, yayin da ambaliyar ta shafi mutane dubu 41 a Birnin Durban .

Birnin Durban biyo bayan ambaliya a Afrika ta kudu
Birnin Durban biyo bayan ambaliya a Afrika ta kudu REUTERS - ROGAN WARD
Talla

Wannan sabon adadin ya fito ne daga Firimiyar Yankin KwaZulu-Natal dake birnin Durban Sihile Zikalala wanda yace a yankin nasu kawai iftila’in ya shafi mutane sama da 40,000, yayin da wasu mutane suka bata.

Tuni gwamnatin kasar ta kafa dokar ta baci sakamakon irin ta’adin da ambaliyar ta haifar na rusa gidaje da karya turakun lantarki da itatuwa da turakun lantarki, yayin da ya wanke tare da zabtare wasu hanyoyin yankin.

wasu daga cikin mutanen da ambaliya ta ritsa da su a Afrika ta kudu
wasu daga cikin mutanen da ambaliya ta ritsa da su a Afrika ta kudu AP - Kopano Tlape

Shugaba Cyril Ramaphosa da ya ziyarci yankunan domin ganewa idon sa da kuma jajantawa wadanda hadarin ya ritsa da su, ya bayyana matukar takaicin sa dangane da girma matsalar wanda masana suka ce an kwashe sama da shekaru 60 basu taba ganin irin wannan ambaliya ba.

Gwamnatin kasar ta kafa sansanoni 17 domin tsugunar da wadanda suka rasa matsugunin su, yayin da jama’a suka fara korafi akan rashin agajin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.