Isa ga babban shafi

Equatorial Guinea ta kame dan fafutukar kare hakkin dan Adam gabanin zabe

Equatorial Guinea ta tsare jagoran wata kungiya ta ''Guinea is also ours'' wadda ta shahara a fagen fafutukar kare hakkin dan Adam a sassan kasar, tsawon kwanaki 18, bayan da ya taimakawa ‘yan adawa a lokacin da ‘yan sanda suka yi wa shalkwatar jam’iyyarsu kawanya, kamar yadda lauyansa da matarsa suka shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Wasu jami'an 'yan sandan Equatorial Guinea.
Wasu jami'an 'yan sandan Equatorial Guinea. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Ma'aikatar shari'ar Equatorial Guinean dai ta ki cewa komai kan rahoton, a lokacin da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya nemi karin bayani.

A ranar 25 ga watan Satumban da ya gabata, aka kama Anacleto Micha Nlang, wanda ya kafa kungiyar kare hakkin mai suna "Guinea is also ours" bayan ya dawo daga ofishin jam'iyyar adawa ta CI, inda ya kai kayan abinci ga iyalan da aka yi wa kawanya a ofisoshin, wadanda suka hada da mata da yara.

Yayin da ya rage kusan wata guda a gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisu da na kananan hukumomi, jami’an tsaro sun kara azama wajen kamen ‘yan adawa, bisa zarginsu da aikata ba dai dai ba.

Gwamnatin shugaba Teodoro Obiang Nguema na  cigaba da shan caccaka daga kungiyoyin fararen hula, bisa zarginta da yin amfani da karfi wajen dakile tasirin ‘yan adawa a Equatorial  Guinea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.