Isa ga babban shafi

Za a sanyawa Mali takunkumi idan ta gaza sako sojojin Ivory Coast - Ecowas

Shugabannin kasashen yammacin Afirka sun shaidawa gwamnatin mulkin sojin Mali da ta sako sojojin Ivory Coast 46 da aka kama a watan Yuli ko kuma a kakaba wa kasar takunkumi.

Shugabannin kungiyar Ecowas kenan yayin wani taro a Abujan Najeriya
Shugabannin kungiyar Ecowas kenan yayin wani taro a Abujan Najeriya © ecowas
Talla

"Muna rokon hukumomin kasar Mali da su sako sojojin Ivory Coast nan da ranar 1 ga watan Junairu, 2023," in ji Omar Alieu Touray, shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, da yake shaidawa manema labarai a wani taro da kungiyar ta gudanar a Abujan Najeriya.

Jami’in diflomasiyyar na kasar Gambia Touray ya kuma ce kungiyar kasashen yammacin Afirka na da damar daukar mataki idan ba a sako sojojin ba nan da ranar 1 ga watan Janairu.

“Idan har Mali ta gaza yin hakan, Ecowas za ta kakaba mata takunkumi,” in ji Omar Alieu Touray.

Ecowas ta ce, shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe, wanda ke shiga tsakani tsakanin Mali da Ivory Coast kan wannan batu, zai je kasar Mali domin neman a sako sojojin.

A ranar 10 ga watan Yuli ne aka kame sojojin na Ivory Coast a lokacin da suka isa filin jirgin saman Bamako babban birnin kasar Mali.

Ivory Coast ta ce an aike da sojojin ne domin ba da tallafi ga tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Mali, MINUSMA, kuma ana tsare da su ne yanzu haka a kasar ba bisa ka'ida ba.

Kasar Mali ta ce sojojin haya ne aka tura mata, kuma aka tura su gidan yari bisa zargin yunkurin gudanar da zagon kasa ga sha’anin tsaron kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.