Isa ga babban shafi

Mayakan Al Shebaab sun kashe mutane 5 a Mogadishu

Fararen hula biyar sun rasa rayukansu a lokacin da mayakan kungiyar al-Shabab suka tayar da bam, tare da bude wuta kan ginin gwamnati a Mogadishu babban birnin kasar Somalia.

Jami'an tsaron Somalia na rike da makamansu kusa da ofishin magajin gari bayan hare-haren da mayakan Al Shebaab suka kai a Mogadishu, babban birnin kasar Somalia. 22 ga Janairu, 2023.
Jami'an tsaron Somalia na rike da makamansu kusa da ofishin magajin gari bayan hare-haren da mayakan Al Shebaab suka kai a Mogadishu, babban birnin kasar Somalia. 22 ga Janairu, 2023. © REUTERS/Feisal Omar
Talla

Ma'aikatar yada labaran kasar ta ce mayakan sun kaddamar da farmaki ne kai tsaye kan ginin da ofishin magajin garin Mogadishu yake, da tsakar ranar Lahadi,  inda suka yi artabu da jami’an tsaro.

Bayan shafe tsawon lokaci suna fafatawar, jami’an tsaro suka kashe ‘yan kungiyar guda shida tare da fatattakarsu da misalin karfe 6 na yamma, kamar yadda ma’aikatar yada labaran kasar ta Somalia ta wallafa a shafinta na Facebook.

Babban jami’in hukumar bayar da agajin gaggawa a kasar Abdikadir Abdirahman, ya ce mutane 16 suka jikkata a harin.

A watannin baya bayan nan dai Al-Shabaab ta kara yawan hare-haren da take kaiwa a sassan Somalia, tun bayan da gwamnatin shugaba Hassan Sheikh Mohamud ta kaddamar da farmakin neman murkushe kungiyar da ke da alaka da al-Qaeda a watan Agusta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.