Isa ga babban shafi

Shugaban kasar China zai gana da shugabannin kasashen Afirka a taron BRICS

Shugaban kasar China Xi Jinping, zai gana da shugabannin kasashen Afirka a gefen taron BRICS a mako mai zuwa, a wani matyaki na bunkasa alakar China da Afirka.

Shugaban China China Xi Jinping kenan a wani taron BRICS da ya gudana a Afirka ta Kudu ranar 26 ga watan Yuli, 2018.
Shugaban China China Xi Jinping kenan a wani taron BRICS da ya gudana a Afirka ta Kudu ranar 26 ga watan Yuli, 2018. REUTERS - POOL
Talla

Za a yi taron ne da yammacin ranar Alhamis, wato ranar karshe ta taron na kwanaki uku, in ji Chen Xiaodong jakadan China a Afirka ta kudu a wani taron manema labarai.

An kebe ranar ne domin gudanar da bukukuwan da suka hada da kasashe sama da 70 da aka gayyata a matsayin aminan kungiyar BRICS, wadanda suka hada da Brazil, Rasha, Indiya, China da Afirka ta Kudu.

A ranar Talata, Xi zai kai ziyarar aiki ga shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a birnin Pretoria, daga bisani kuma ya wuce birnin Johannesburg don halartar taron, wanda zai kasance ziyararsa ta biyar a Afirka ta Kudu tun bayan da ya zama shugaban kasa a shekarar 2013.

Mu'amalar kasar China da shugabannin Afirka za ta biyo bayan taron Rasha da Afirka da aka yi a watan da ya gabata a birnin St Petersburg, inda shugaba Vladimir Putin ya gudanar da taron koli da shugabannin kasashen Afirka 17 da suka halarci taron daga cikin kasashen Afirka 54 da aka gayyata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.