Isa ga babban shafi

Madagascar ta haramtawa jam'iyyun adawa 11 gangamin yakin neman zabe

Gwamnatin Madagascar ta dakile jam’iyyun adawa 11 daga gudanar da gangamin kaddamar da yakin neman zaben shugabancin kasar da suka shirya yi a yau Asabar.

Guda cikin 'yan takarar jam'iyyar adawa a Madagascar, Siteny Randrianasoloniako.
Guda cikin 'yan takarar jam'iyyar adawa a Madagascar, Siteny Randrianasoloniako. © Equipe de campagne du candidat
Talla

Jam’iyyun adawar 11 sun shirya fara gangamin gabatar da ‘yan takararsu gaban dubban magoya baya a katafaren filin wasanni na Palais des Sports da ke babban birnin kasar Antannanarivo.

Matakin dakile ‘yan adawar daga gangamin dai na da nasaba da yunkurin kalubalantar hukuncin kundin tsarin mulkin kasar da ta bai wa shugaba Rajoelina damar tsayawa takara don neman sabon wa’adin mulkin kasar.

Tuni dai kotun ta yi watsi da bukatar hadakar da bangaren adawar ya shigar, wanda ke nuna cewa Rajaolina zai shiga sahun ‘yan takara 14 da za su fafata a babban zaben da ke tafe.

Dan takarar shugaban kasa Hajo Andrianainarivelo, ya ce idan har gwamnati ba ta basu damar gudanar da gangamin a filin wasannin ba, kai tsaye za su koma gudanar da gangamin siyasar su a tsakar tituna don ceto demokradiyyar kasar.

An dai wayi gari da ganin dandazon sojoji baibaye a gab da kofar shiga babban filin wasan dukkaninsu dauke da manyan makamai, duk kuwa da yadda bangaren adawar suka nemi izini gaban shirya gangamin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.