Isa ga babban shafi

Mayakan Azawad sun yi ikirarin kwace iko da karin sansanin sojin Mali

Mayakan Azbinawa a Mali sun yi ikirarin kwace karin sansanin sojin kasar na Bamba, bayan fafatawar da suka yi da dakarun gwamnatin, ranar Lahadi a garin Gao da ke arewacin kasar.

Wasu mayakan Azbinawa da ke fafutukar ballewar yankin Azawad daga Mali.
Wasu mayakan Azbinawa da ke fafutukar ballewar yankin Azawad daga Mali. REUTERS/Souleymane Ag Anara
Talla

Kakakin kungiyar ‘yan tawayen na Azawad, Mohamed Elmououd Ramadane ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Sansanin na Bamba dai shi ne na hudu da mayakan na Azawad suka yi ikirarin kwacewa, tun bayan hare-haren da suka kaddamar a cikin watan Agustan da ya gabata, bayan ficewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya daga Mali.

Sai dai cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta na X, rundunar sojin Mali cewa ta yi dakarunta  na ci gaba da yin gumurzu da mayakan Azbinawan a yankin na Bamba, inda ta ce a nan gaba za ta yi karin bayani kan halin da ake ciki.

Kafin ikirarin kwace sansanin sojin Mali na Bamba dai, sai da ‘yan tawayen da ke neman kafuwar yankin Azawad suka kwace iko da sansanonin soji uku da ke Lere, da Dioura da kuma Bourem a cikin makwannin da suka gabata.

Azbinawan masu neman ballewar yankinsu na Azawad daga Mali, wadanda a shekarar 2015 suka ajiye makamansu bayan kulla yarjejeniya da gwamnati, sun dade suna korafin cewar mahukuntan kasar na yin watsi da mutunta sulhun da suka yi.

A shekarar 2012 ne dai ‘yan tawayen suka fara tayar da kayar baya kafin daga bisani sojojin Faransa su taimaka wajen fatattakarsu daga manyan biranen da suka kame.

A waccan lokacin, mayakan ‘yan ta’adda sun ribaci tawayen na Azawad, inda suka yi amfani da damar wajen fara kai hare-hare kan jami’an tsaro da fararen hula a sassan Mali, lamarin da da ya janyo salwantar rayukan mutane da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.