Isa ga babban shafi
YANKIN SAHEL

Macron da Ouattara sun tattauna kan juyin mulkin Nijar

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron da takwaransa na Ivory Coast, Alassane Ouattara sun tattauna kan halin da matsalar tsaro ke ciki a yankin Sahel, da kuma batun juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar, yayin wata ganawa da suka yi a birnin Paris.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron kenan, lokacin da yake karbar bakuncin takwaransa na Côte d'Ivoire, Alassane Ouattara a birnin Paris.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron kenan, lokacin da yake karbar bakuncin takwaransa na Côte d'Ivoire, Alassane Ouattara a birnin Paris. AFP - IAN LANGSDON
Talla

Haka zalika shugabannin biyu sun tattauna kan harkokin cikin gida da ke faruwa a Ivory Coast, bayan babban zaben kasar da aka gudanar a cikin watan Satumba, wanda jam’iyyar Ouattara ta samu nasara a kai.

Shugabannin sun tattauna kan ayyukan soji na hadin gwiwa da kuma alakar kasuwanci, musamman a bangaren makamashi da kuma samar da ci gaba mai dorewa.

Ko da yake tattaunawar ta su ta fi mayar da hankali ne kan halin matsalar tsaron da yankin Sahel ke ciki, da kuma juyin mulkin Nijar da ke neman kawo rarrabuwar kawuna a yankin Yammacin Afirka.

Faransa da ta yi wa wadannan kasashe mulkin mallaka, ta kafa sansanin soji a yankuna da dama na nahiyar Afirka, musamman a kasashen Chadi, Snegela, Gabon, Djibouti da kuma Ccte d'Ivoire.

Macron dai ya jaddada goyon bayansa ga matakin kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka, tare da alwashin nemo mafita kan halin da mulkin Nijar ke ciki.

Kungiyar bunkasa tatta;lin arzikin kasashen Yammacin Afirka, ta sanya takunkumi akan Nijar, tare da barazanar amfani da karfin soji wajen dawo da tsarin kundin tsarin mulkin kasar, idan har ta gaza cimma jituwa da shugabannin mulkin soji, inda kasar Cote d'Ivoire ta ce a shirye take da ta tura bataliyar sojojinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.