Isa ga babban shafi

Rahoton MDD ya tabbatar da goyon bayan Rwanda ga mayakan M23 a Jamhuriyar Congo

Wani rahoto da tawagar kwararru ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ya nuna cewa, sojojin kasar Rwanda sun kaddamar da farmakin soji kan sojojin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo a gabashin kasar da ke fama da rikici.

yadda mazauna Goma wato birnin Arewacin Kivu ke ficewa daga gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, bayan da mayakan M23 suka farwa yankin a watan Oktoban 2023.
yadda mazauna Goma wato birnin Arewacin Kivu ke ficewa daga gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, bayan da mayakan M23 suka farwa yankin a watan Oktoban 2023. © Alexis Huguet, AFP
Talla

Kwararrun sun ce akwai kwararan hujjoji da ke nuna cewa sojojin Rwanda na tsoma baki kai tsaye da kuma goyon ga 'yan tawayen M23 na yankin, musamman bangaren da ya shafi makamai, alburisai da kuma kaki.

Rahoton na zuwa ne a daidai lokacin da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ke ci gaba da bayyana zargin Rwanda da mara wa kungiyar M23 baya.

Mayakan sun kwace yankuna da dama a gabashin Congo tun bayan da kasar ta fada cikin tashin hankali.

Kasar Rwanda ta sha musanta cewa tana goyon bayan ‘yan tawayen, amma Amurka da Faransa da sauran kasashen yammacin duniya sun amince da rahoton da Jamhuriyar Congo ta fitar.

A cewar rahoton kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya, sojojin Rwanda sun shiga tsakani don karfafa kungiyar ta M23 da kuma yaki da 'yan kabilar Hutu masu tsattsauran ra'ayi na Rwanda wadanda suka aiwatar da kisan kiyashi na Tutsi a shekarar 1994.

Kungiyar da ke karkashin jagorancin 'yan Tutsi, wato M23 kenan ta fara yin fice a duniya a lokacin da ta kwace birnin Goma na gabashin Congo a shekara ta 2012 kafin daga bisani aka fatattake su a shekara 2013.

Tuni dai kungiyar ta M23 ta kwace yankuna da dama a gabashin lardin Kivu ta Arewa da ke kan iyaka da kasar Rwanda, tare da raba dubban mutane da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.