Isa ga babban shafi

Burundi ta kulle iyakarta da Rwanda kan zargin Kigali da goyon bayan 'yan tawaye

Burundu ta dauki matakin kulle iyakar da ke tsakaninta da da Rwanda bayan tabarbarewar alakar da ke tsakanin kasashen biyo makwabtan juna, inda Burundin ke zargin makwabciyar tata da taimakon ‘yan tawayen kasar.

Wannan ba shi ne karon farko da Burundi ke kulle iyakar da ke tsakaninta da Rwanda ba.
Wannan ba shi ne karon farko da Burundi ke kulle iyakar da ke tsakaninta da Rwanda ba. AFP/Stéphanie Aglietti
Talla

A jawabin da ya gabatar ta gidan talabijin bayan daukar matakin, ministan cikin gida na Burundi Martin Niteretse ya ce Burundi za ta dakatar da duk wata alaka da ke tsakaninta da Rwanda har sai Kigali ta sauya matsayarta kan tallafawa ‘yan tawaye.

Wannan dai ne zarge-zarge na baya-bayan nan da ke alakanta Rwandan da tallafawa ko kuma daukar nauyin ‘yan tawayen na Burundi kacokan.

Tun cikin watan Disamban bara shugaba Évariste Ndayishimiye na Burundi ya zargi Rwandar da daukar nauyin ‘yan ta’addan bayan da suka kashe mutane 20 a iyakar da ta hada Burundi da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Shugaba Paul Kagame na Rwanda ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake yiwa gwamnatinsa na daukar nauyin ‘yan tawayen wadanda ke kai munanan hare-hare, yayinda ya bayyana takaicinsa da matakin Burundi na kulle iyakar.

Kungiyar ‘yan tawayen Red Tabara ta dauki alhakin hare-haren na watan Disamba wanda ya kashe sojoji 9 da dan sanda guda.

Kungiyar ta Red Tabara na gudanar da ayyukanta ne daga yankin Kivu na kudancin Congo mai iyaka da Burundi da nufin kalubalantar gwamnatin kasar.

Wannan da iba shi ne karon farko da Burundi ke kulle iyakar da ke tsakaninta da Rwanda ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.