Isa ga babban shafi

UNICEF ta bukaci gaggauta samar da tsaro a fadin makarantun Najeriya

Hukumar Kuala da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ta yi Allah-wadai da ayyukan ‘yan bindiga na kwanan nan da suka yi sanadiyar sace yara ‘yan makaranta sama da 200 a Jihar Kaduna.

Hoto don mislai.
Hoto don mislai. © UNICEF
Talla

A ranar Alhamis da ta gabata ne wasu 'yan bindiga suka kai hari wata makaranta da ke kauyen Kuriga a jihar Kadunan Najeriya, inda suka kwashe sama da dalibai 200.

Wakiliyar UNICEF a kasar, Cristian Munduate, a wata sanarwa da ta fitar, ta ce yawaitar hare-haren da ake kai wa cibiyoyin ilimi a fadin kasar na nuni da cewa wannan, matsala ce da ke bukatar daukar matakin gaggawa daga dukkan matakai na gwamnati da na al'umma.

Ta bukaci daukar matakin gaggawa don ganin an dawo da yaran da ma’aikatan da aka sace, tare da yi kira ga hukumomi da su aiwatar da kwararan matakai na tabbatar da tsaro dukkan makarantu a fadin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.