Isa ga babban shafi
Nijar - Ambaliya

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane fiye da 60 a Nijar

Adadin wadanda ambaliyar ruwa ta halaka a Jamhuriyar Nijar sakamakon saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya ya karu zuwa mutane 64.

Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wasu sassan Jamhuriyar Nijar.
Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wasu sassan Jamhuriyar Nijar. © Tchadinfos.com
Talla

Tun cikin watan Yulin da ya gabata sassan Jamhuriyar Nijar ke fuskantar saukar mamakon ruwan saman da ya haddasa ambaliya

Kididdigar baya bayan nan da hukumomin kasar suka fitar ta ce masifun ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa sun shafi mutane kusan dubu 70 a fadin kasar, tare da lalata gidaje sama da dubu 5.

Yankunan da ambaliyar ta fi shafa sun hada Maradi, Agadez, da Yamai babban birnin kasar.

A gefe guda kuma ma’aikatar lafiyar Nijar din ta ce aukuwar iftila’in na ambaliya ya janyo barkewar cutar kwalara wadda kawo yanzu ta kashe mutane 16.

A shekarar 2020, ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar mutane 73, gami da tagayyara mutane kimanin miliyan 2 da dubu 200, kamar yadda rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.