Mahamadou Issifou ya karbi kyautar dala milyan biyar daga gidauniyar Mo Ibrahim a Kenya
A birnin Nairobi na kasar Kenya, an gudanar da taron shekara-shekara na gidauniya mai suna Mo Ibrahim dake mayar da hankali kan shugabanci na gari a karkashin tsarin dimokuradiyya tare da shirya sahihin zabe bisa turbar dimokuradiyya.
Wallafawa ranar:
Taron da aka soma a jiya juma’a a Nairobi ya hada manyan yan siyasa da Shugabani,inda tsohon Shugaban Nijar Mahamadu Issifou wanda ya lashe kyauta daga wannan gidauniya ya kuma karbi labar yabo da kyauta ta dala milyan biyar na shekara ta 2021 daga hannun wannan gidauniya.
A lokacin da ya ke jawabi yan lokuta da karbar wannan kyauta ,tsohon Shugaban na Nijar ya koka dangane da halin rashin tsaro da wasu kasashe Afirka suka tsunduma,ya kuma yi misali da kasashen Mali,Burkina Faso,Guinea Conakry sai wannan sabon yaki da ya barke a Sudan.
Tsohon Shugaban na Nijar ya bukaci shugabanin kasashe da Majalisar Dimkin Duniya su tashi tare da daukar matakan da suka dace don kawo karshen wannan al'amari na juyin mulki da yake-yake da ke wakana a Afirka da wasu yankuna daban.
Baya ga haka mahalarta taron za su tattaunawa tare da mayar da hankali ne kan taken matsayin Afirka a duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu