Isa ga babban shafi

A karon farko tawagar ECOWAS ta gana da Bazoum

Tawagar kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS, ta samu nasarar ganawa da hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum.

Bazoum Mohamed  lokacin da tawagar ECOWAS ta ziyarce shi a inda yake tsare
Bazoum Mohamed lokacin da tawagar ECOWAS ta ziyarce shi a inda yake tsare © Nigeria Presidency
Talla

A cewar wakilin gidan Talabijin na France 24, an gudanar da ganawar ce a gaban Firaministan kasar da sojojin da suka yi juyin mulki a kasar suka nada, Ali Mahaman Lamine Zeine.  

A ziyarar farko da tawagar ta kai kasar a cikin wannan wata, sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun ki basu damar ganawa da Bazoum.

Toh sai dai nasarar ganawar a yanzu, ita ce ta biyu da wata tawaga ta yi da shi, tun bayan hambarar da gwamnatinsa da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan da ya gabata.

A yau ne Asabar ne dai tawagar ta ECOWAS da ke karkashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soji a Najeriya, Janar Abdulsami Abubakar, da mai alfarma Sarkin Musulmi na kasar Muhammad Sa’ad Abubakar, suka sake komawa kasar don gudanar da tattaunawa gameda juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.

Ziyarar na zuwa ne kwana guda bayan kammala taron hafsoshin sojojin kasashen da ke karkashin kungiyar ECOWAS da ya gudana a Ghana, inda suka bayyana aniyarsu ta yin amfani da karfin soji wajen maida gwamnatin farar hula, muddin sojojin Nijar din suka ci gaba da yin turjiya gameda matakan diflomasiya da ECOWAS ke dauka don warware rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.