Isa ga babban shafi

Kasashen waje ke amfana da kungiyar G5 Sahel - Yan Nijar

Burkina Faso da Nijar sun fice daga kungiyar G5 Sahel dake yaki da ayyukan ta’addanci a Sahel ; a ranar Asabar 2 ga watan Disamba ne kasashen suka  sanar da ficewa daga kungiyar G5 Sahel kamar dai yada kasar  Mali ta yi a watan Mayu. 2022.

Yankin Sahel mai fama da ta'addanci
Yankin Sahel mai fama da ta'addanci AP - Leo Correa
Talla

Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso tun daga ranar 29 ga watan Nuwamban 2023, a cikin wata sanarwar ga manema labarai,tun vayan samar da wannan kungiyar a shekara ta  2014, da nufin yakar ta’adanci a Sahel,kasashen  Mali, Burkina Faso, Nijar, Mauritania da Chadi sun kudiri aniyar aiki tare tareda tallafin kasashen waje,Wanda ga baki daya yan kasar ta Nijar suka bayyana cewa an kasa cimma burin da aka saka gaba

Nuhu Arzika daya daga cikin masu aiki da kungiyoyin fararen hula ya na mai bayana cewa kungiyar ta G5 bayan kokawa da rashin kayan aiki da isasun kudin aiki ta kasa kawo karshen ayyukan ta’adanci a yankin ga baki daya.

Dakarun G5 Sahel
Dakarun G5 Sahel AP - Jerome Delay

A watan Mayun 2022, kasar Mali, a karkashin mulkin soja ta sanar da ficewa daga wannan kungiya ta G5, Hukumomin Sojin Mali na  ikirarin cewa “kasashen waje ne ke amfana da kungiyar".

Bayan ficewar kasashen Nijar da Burkina Faso, Kasashen Chadi da Mauritania a yau Laraba sun bayyana cewa babu abinda ya rage daga gare su banda  su fice daga kungiyar Wanda hakan za ya kai ga rusa kungiyar ta G5 Sahel ga baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.