Isa ga babban shafi
Colombia

An rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya a Colombia

Gwamnatin Colombia da ‘yan Tawayen kasar, sun rattaba hannu akan sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya a wani biki da akayi a Bogota, duk da adawar da hakan da wasu ‘yan kasar keyi.

Shugaban Colombia Juan Manuel Santos yayin jawabi bayan rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan tawayen FARC
Shugaban Colombia Juan Manuel Santos yayin jawabi bayan rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan tawayen FARC
Talla

Shugaban kasar Juan Manuel Santos da shugaban ‘yan tawaye Rodrigo Timochenko Londono ne suka sa hannu a gaban daruruwan ‘yan kasar, da wani alkalami da aka kera daga harsashin da akayi amfani da shi a yakin da shafe tswon lokaci ana fafatashi a kasar.

Shugaba Santos ya shaidawa taron cewa, kowa ya san barnar da yakin da aka kwashe dogon lokaci ana yi ya haifar, saboda haka ya zama wajibi a rungumi zaman lafiya.

Ana saran gabatarwa Majalisar kasar sabuwar yarjejeniyar, domin amincewa da ita.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.