Isa ga babban shafi
FIFA

FIFA ta tsayar da ranar zaben sabon shugaba

Shugaban FIFA hukumar da ke kula da sha’anin kwallon kafa a duniya Sepp Blatter a jiya litinin ya tabbatar da cewa ba zai sake tsaya wa takarar shugabancin hukumar ba. Blatter ya fadi haka ne a taron shugabannin hukumar FIFAda aka gudanar a Zurich.

An watsa wa Blatter kudaden jabu
An watsa wa Blatter kudaden jabu REUTERS/Arnd Wiegmann
Talla

Shugabannin hukumar sun tsayar da ranar 26 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za’a gudanar da zaben wanda zai gaji Blatter.

Akwai kuma kwamiti na musamman da aka kafa wanda zai gaggauta samar da sabbin sauye sauye domin tsabtace hukumar da cin hanci da rashawa ya bata wa suna,

Wani batu da ya ja hankali a zauren taron shi ne yadda wani mai barkwanci Dan Birtaniya ya watsa wa Blatter kudaden jabu na daloli, a lokacin da shugabann na FIFA ke amsa tambayoyin ‘Yan Jarida kan badakalar cin hanci da ta dabaibaye FIFA.

Tun a 1998 Blatter ke jagorantar FIFA, kuma a ranar 29 ga watan Matu ya lashe zabensa wa’adi na biyar duk da a lokacin ne aka bankwado zarge zargen cin hanci karkacin jagorancinsa

Wannan ne kuma ya tursasawa Blatter yin murabus daga mukaminsa.

Yanzu haka kuma wata majiya da ke kusa da Michel Platini babban mai adawa da Blatter ta kwarmato cewa nan da mako biyu shugaban hukumar Kwallon Turai zai bayyana kudirin ko zai tsaya tsakarar shugabancin FIFA.

FIFA ta ba masu son takarar shugabancin FIFA daga nan zuwa ranar 26 a watan Oktoba su mika sunayensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.