Isa ga babban shafi
wasanni

Manyan jami'an Barcelona sun yi murabus saboda Catalonia

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Josep Maria Bartomeu ya tabbatar cewa, mutane biyu daga cikin mambobin kwamitin zartaswar kungiyar sun yi murabus saboda matakin da ya dauka na bada umarnin buga wasa a bayan fage.

Barcelona ta fafata da Las Palmas a sirce don nuna bacin rai kan yadda jami'an Spain suka  ce sun murkushe masu kada kuri'ar raba gardama
Barcelona ta fafata da Las Palmas a sirce don nuna bacin rai kan yadda jami'an Spain suka ce sun murkushe masu kada kuri'ar raba gardama REUTERS/Albert Gea
Talla

Barcelona ta fafata da Las Palmas a gasar La Liga a filinta na Camp Nou ba tare da barin magoya bayanta sun shiga filin wasan ba, a wani mataki na nuna bacin rai kan abin da ta kira murkushewar da jami’an tsaro suka yi wa mutanen yankin Catalonia da suka fito don kada kuri’ar raba gardama dangane da ballewar yankin daga Spain.

Mataimakin shugaban kungiyar ta Barcelona, Carles Vilarrubi da kwamishinan ayyukan ci gaban kungiyar Jordi Mones sun mika takardar ajiye aikinsu saboda adawarsu da buga wasan a sirce.

Su dai mutanen biyu sun zabi a kaurace wa buga wasan baki daya ko da hakan zai kai ga hukunta kungiyar ko kuma a cita tara.

A bangare guda, yau ne ake saran Barcelon za ta shiga cikin yajin aikin game- gari da yankin na Catalonia ya kira don nuna adawa da abin da ya kira keta hakkin jama'arsa a zaben na raba gardama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.