Ganduje ya bukaci Fulani su koma Kano da kiwo
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci daukacin Fulani makiyaya da ke sassan Najeriya musamma a jihohin Benue da Taraba da su koma Kano don ci gaba da kiwon dabbobinsu.
Wallafawa ranar:
Gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya ce, jiharsa na da manyan filayen kiwo da za su karbi makiyayan da dabbobinsu.
Ganduje ya bayyana haka ne a yayin sanya ido a shirin rigakafin cutukan dabbobi musamman shanu sama da miliyan 1 a karamar hukumar Garum Malam da ke jihar.
Ganduje ya kuma yi Allah Wadai da rikicin Fulani makiyaya da manoma na baya-bayan da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a sassan kasar, in da ya ce, dole ne a kawo karshen kisan da ake danganta wa Fulani
Daga cikin wuraren da Ganduje ya ce za su karbi Fulanin da ya gayyata, sun hada da Gaya da Rogo da Kura da Tudun Wada da Ungoggo, in da ake da manyan filayen noma da kiwo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu