Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya dora laifin kashe-kashe a Najeriya kan Gaddafi

Shugaba Muhammadu Buhari ya dora laifin kashe-kashen da ake fama da su a Najeriya akan marigayi Mu’ammar Gaddafi, tsohon shugaban kasar Libya da ya rasu shekaru bakwai da suka gabata.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da wani babban jagoran addinin Kirista a birnin London, Archbishop Justin Webly na Canterbury, in da ya ce, makaman da marigayin ya bai wa magoya bayansa, sune aka yi safarar su cikin Najeriya har ake amfani da su wajen kashe mutane a yau.

Rahotanni sun ce, gabanin mutuwarsa, Mr. Gaddafi da aka kifar da gwamnatinsa tare da taimakon kasashen Yammacin duniya, ya samar da makamai masu tarin yawa ga magoya bayansa don yakar masu yi masa tawaye.

A cewar shugaba Buhari, wadannan ‘yan bindigar sun samu horo daga Gaddafi, sannan bayan mutuwarsa ne suka tsere da makaman da ke hannunsu, in da suka bazu a kasashen da ke yankin kudu da Sahara.

Buhari ya kara da cewa, sun gano ire-iren wadannan mayakan a cikin kungiyar Boko Haram.

Baya ga matsalar Boko Haram da ta lakume rayuka a Najeriya, har ila yau rikicin manoma da makiyaya sun haddasa asarar daruruwan rayuka a kasar.

Gaddafi da aka kashe a cikin watan Oktoban shekarar 2011, ya jagoranci Libya na tsawon shekaru 42, yayin da rikicin tsawon makwanni ya yi sanadiyar kifar da gwamnatinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.