Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta hana Gwamnan Yobe kada kuri'a

Kungiyar Boko Haram ta hana Gwamnan Jihar Yobe, Ibrahim Gaidam kada kuri’arsa a zaben shugabancin Najeriya da ake gudana a wannan Asabar.

Gwamnan Yobe Ibrahim Gaidam.
Gwamnan Yobe Ibrahim Gaidam. Daily Post
Talla

Wata sanarwa da ofishin jami’in hulda da manema labarai na Gaidam ya fitar, ta bayyana cewa, Gwamnan ya yanke shawarar janyewa daga kada kuri’arsa ne sakamakon hare-haren da kungiyar ta kaddamar a wasu wurare biyu a sanyin safiyar yau.

Sanarwar ta ce, Gwamnan ya gaza tafiya zuwa mazabarsa ta Bukarti da ke kusa da garin Gaidam mai nisan kilomita 230 daga babban birnin Jihar.

Rahotanni sun ce, hankula sun kwanta a yanzu, yayin da tuni aka fara fitar da sakamakon zaben a wasu wurare daban daban da ke sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.