Chelsea za ta kai matakin gaba a gasar Turai- Hiddink
Kocin Chelsea, Guus Hiddink ya yi amanna cewa, kungiyarsa na da damar kai wa matakin wasan dab da na kusan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai kamar yadda PSG ke da irin wannan damar, duk da cewa PSG din ta doke ta da ci 2-1 a jiya talata.
Wallafawa ranar:
A karawarsu ta jiya, PSG ce ta fara zura kwallo ta hannu Zlatan Ibrahimovic a minti na 39 amma daga bisani Mikel Obi na Chelsea ya barke kwallon a minti na 45.
To sai kuma, Edison Cavani na PSG ya samu nasarar zura kwallo guda, lamarin da ya bai wa PSG damar doke Chelsea da ci 2-1.
A karo na biyu kenan da Mikel Obi, dan asalin kasar Najeriya ya ci wa Chelsea kwallo a gasar zakarun Turai, amma a jumulce, sau shida kenan cikin kusan shekara 10 da ya ciwa Chelsea din kwallo.
Sannan a karon farko kenan da Chelsea ta yi rashin nasara tun bayan da ta nada Guus Hiddink a matsayin sabon kocinta bayan ta kori Jose Mourinho a watan Disamban bara.
A ranar 9 ga watan Maris mai zuwa kungiyoyin biyu za su sake kece raini a filin wasa na Stamford Bridge.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu