Isa ga babban shafi
Wasanni

Rasha: Ighalo ya soki tsarin mai horar da Super Eagles

Dan wasan gaba na Najeriya, Odion Ighalo, ya ce bai ji dadin yadda ya buga wasan da suka fafata da kaasar Croatia ba, inda ya zama shi kadai ne tilo mai jefa kwallo na tawagar Super Eagles.

Dan wasan gaba na Najeriya Odion Jude Ighalo a (dama), tare da dan wasan Croatia Ante Rebic yayinda suka yi tsalle a wasan gasar cin kofin duniya rukuni na D, da suka fafata a ranar Asabar 17, Yuni, 2018.
Dan wasan gaba na Najeriya Odion Jude Ighalo a (dama), tare da dan wasan Croatia Ante Rebic yayinda suka yi tsalle a wasan gasar cin kofin duniya rukuni na D, da suka fafata a ranar Asabar 17, Yuni, 2018. OZAN KOSE / AFP
Talla

Ighalo ya bayyana haka ne, yayin da yake sukar tsarin rarraba ‘yan wasa da mai horar dasu Gernot Rohr ya zaba, na sanya ‘yan wasa uku a baya, biyu a gabansu, uku a tsakiya sai kuma jefa kwallo daya a gaba, wato 3-2-3-1, sabanin tsarin da aka saba gani na hudu a baya, hudu a tsakiya, da kuma masu jefa kwallo biyu a gaba; 4-4-2.

Korafin na Ighalo na zuwa ne bayanda tsohon gwarzon dan wasan Najeriya Jay Jay Okocha ya dora alhakin kayen da Najeriya ta sha akan rashin dabara.

Okocha, ya ce mai horar da ‘yan wasan Najeriyar ya sauya musu guraben da suka saba buga wasanni a kai, dalilin da ya hanasu tabuka wani abin azo a gani.

Tsohon dan wasan na Super Eagles ya bayar da misalin cewa kama ta yayi, kaftin din tawagar Super Eagles Mikel Obi, ya buga bangaren dan tsakiya mai tsaron gida, kamar yadda ya ke yi a lokacin da yake kungiyar Chelsea, amma ba sashin dan tsakiya mai jefa kwallo ba.

A ranar 22 ga watan Yuni da muke ciki Najeriya za ta fafata da Iceland, yayinda kuma a ranar 26 ga watan za ta buga da Argentina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.