Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

'Yan tawaye sun sace 'yan makaranta 30

Gungun mayakan 'yan tawaye 150 a Sudan ta Kudu da ake zargin magoya bayan Riek Machar ne, sun sace yara 30 daga makarantu biyu a Jihar Amadi da ke kasar.

Dakarun sojin gwamnati a birnin Juba na Sudan ta Kudu
Dakarun sojin gwamnati a birnin Juba na Sudan ta Kudu ALBERT GONZALEZ FARRAN / AFP
Talla

Sai dai kuma mai Magana da yawun Machar, Andrew Kuong ya musanta zargin, tare da nisanta mayakansu aikata hakan.

Sace yaran na zuwa kwanaki biyu bayan da ‘yan tawaye suka saki sojoji yara 145, biyo bayan tattaunawarsu da hukumar UNICEF.

Alkalumman hukumar ta UNICEF ya nuna akalla kananan yara 16,000 ne ke yiwa kungiyoyin ‘yan tawaye daban daban, dama rundunar sojin Sudan ta Kudu aiki a matasayin sojoji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.