Isa ga babban shafi
Tanzania

Magafulli ya soke bikin ranar samun ‘yanci kai a Tanzania

Sabon Shugaban kasar Tanzania John Magufuli ya soke bikin samun yancin kan kasar da ake gudanarwa 9 ga watan Disamba, inda ya bukaci karkata kudin da aka ware dan bikin zuwa wajen kula da lafiyar al’ummar kasar.

Sabon Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magufuli
Sabon Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magufuli REUTERS/Sadi Said
Talla

Shugaban ya ce abin kunya ne irin makudan kudaden da ake kashewa wajen irin wadanan bukukuwa yayin da cutar kwalara na cigaba da kasha al’ummar kasar.

Akalla mutane kusan 5,000 suka kamu da cutar kwalara a watan jiya inda aka samu mutuwar da dama daga cikin su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.