Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Afrika ta kudu za ta fice kotun ICC

Kasar Afirka ta kudu na shirin ficewa daga kotun hukunta manyan laifufuka ta duniya ICC saboda abin da ta kira yadda manufofin kotun ya yi karo da muradun kasar. Sai dai Matakin ya janyo suka daga kungiyoyin kare hakkin bil'adama.

Fatou Bensouda babban mai shigar da kara a Kotun duniya ta ICC
Fatou Bensouda babban mai shigar da kara a Kotun duniya ta ICC REUTERS/Michael Kooren
Talla

Rahotanni sun ce, Ministar kula da harkokin kasashen waje Maite Nkoana-Mashabane ta gabatar da takardar ficewar kasar daga kotun a ranar laraba, amma Majalisar Dinkin Duniya ba ta yi karin bayani akai ba.

A bara, Afirka ta kudu ta gamu da suka bayan ta ki kama shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al Bashir da kotun ke nema, a lokacin da ya ziyarci kasar.

Afrika ta kudu ta ce ta ki kama Al Bashir ne saboda tana ganin ya dace yana da kariya a matsayin shi na shugaban kasa

Kasar Burundi ta sanar janye wa daga cikin kotun, yayin da Kenya da Nimibia ma suka nuna alamun janye wakilcinsu a kotun.

Kasashen Afrika dai sun jima suna sukar kotun ICC da aka kafa a 2002 wacce suke ganin ta koma tamkar Karen farautar kasashen yammaci akan shugabannin Afrika.

Duk da ‘Yar Afrika ce shugabar kotun Fatu Bensouda amma shugabannin na ganin kotun ta fi mayar da hankalinta akan su sabanin wasu shugabannin duniya da suka aikata laifukan yaki musamman ta’asar da aka yi a Iraqi zamanin yaki da Saddam Hussian.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.