Isa ga babban shafi
Kenya

Zaben Kenya: Tashin hankali ya barke a yankunan 'yan adawa

‘Yan sandan kasar Kenya sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye, wajen tarwatsa dandazon masu zanga-zanga, da ke jifa da duwatsu da kona tayoyi, a wasu yankunan da ‘yan adawa ke da rinjaye.

Wasu daga cikin magoya bayan jagoran 'yan adawa Raila Odinga, a yankin Kibera da ke birnin Nairobi, yayinda suke tserewa 'yan sandan kwantar da tarzoma da ke kokarin tarwatsa su, 26  ga watan Oktoba 2017.
Wasu daga cikin magoya bayan jagoran 'yan adawa Raila Odinga, a yankin Kibera da ke birnin Nairobi, yayinda suke tserewa 'yan sandan kwantar da tarzoma da ke kokarin tarwatsa su, 26 ga watan Oktoba 2017. REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Rahotanni sun ce tashin hankali ya barke, a yankin Kibera da ke birnin Nairobi, da kuma birnin Kisumu da ke yammacin kasar ta Kenya, inda magoya bayan jagoran ‘yan adawa Raila Odinga suka datse manyan hanyoyi, hakan ya sa da dama daga cikin rumfunan zabe a yankunan kauracewa budewa saboda fargabar abinda zai biyo baya.

Sai dai an cigaba da kada kuri’a a yankunan da ke goyon bayan shugaba mai ci, Uhuru Kenyatta, ko da yake mutane kalilan ne suka fita rumfunan zaben, idan aka kwatanta da zaben farko na watan Agusta.

Arrangamar na zuwa yayinda aka bude rumfunan zabe da safiyar yau Alhamis, domin bai wa masu kada kuri’a miliyan 19, damar sake kada kuri’unsu, a zaben shugaban kasa da kotun kolin kasar ta bada umarnin sake shi, bayan soke wanda ya gudana a ranar 8 ga watan Agusta.

A waccan lokacin dai shugaba mai ci Uhuru Kenyatta ne hukumar zaben kasar ta bayyana a matsayin wanda ya yi nasara.

Sai dai bayan garzayawa kotu, jagoran ‘yan adawa Raila Odinga ya yi nasarar gamsar da kotun kolin kasar ta soke zaben, saboda kura-kurai, da kuma magudin da ta ce an tafka.

Kafin wannan lokacin ne dai, Odinga ya janye daga sake tsayawa takara, tare da kira ga daukacin magoya bayansa da su kauracewa zaben, saboda rashin gamsuwa da yadda tsarin tafiyar da ayyukan hukumar shirya zaben, inda ya ce tilas a yi wa hukumar zaben garambawul kafin ya sake tsayawa takarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.