Isa ga babban shafi

China zata karar da jakunan Duniya nan da shekaru 5 - Rahoto

Wani rahotan binciken masana ya nuna cewar karuwar bukatar Fatun Jakuna da kasar China ke da shi, domin yin magunguna na iya kawar da rabin jakunan da ake da shi a Duniya nan da shekaru 5 masu zuwa.

Yadda ake amfani da jakuna a yankunan Sahel
Yadda ake amfani da jakuna a yankunan Sahel ©AFP/PASCAL GUYOT
Talla

Rahotan yace kusan fatun jakuna miliyan 5 China ke amfani da shi kowace shekara domin yin wani magani da ake kira ‘ejiao’ wanda Yan kasar suka yi imanin cewar yana maganin bukatu da dama da suka hada da sanyin da masu yawan shekaru ke fama da shi.

Rahotan yace shi wannan magani da ada Sarakuna kawai ke amfani da shi, yanzu haka ya samu karbuwa sosai daga jama’a da dama, yadda ake samun karuwar bukatar sa da kashi 20 kowacce shekara daga shekarar 2013 zuwa 2016.

Shugaban kungiyar da ta jagoranci binciken Mike Baker yace wannan bukata ta sa jakunan da China ke da su sun ragu da kashi 76 daga shekarar 1992 zuwa yanzu, abinda ya sa ta mayar da hankali wajen sayo su daga kasashen dake Kudancin Amurka da Afirka da kuma Asia.

Baker yace yanzu haka ana da jakunan da suka kai sama da miliyan 45 a duniya, amma rashin daukar matakan kare su na iya bada damar kawar da su daga doron kasa baki daya.

Rahotan yace wannan bukata daga China ta sa an shigar satar jakunan ana sayar da su, abinda ke barazana ga rayuwar mutane akalla miliyan 500 da suka dogara da su wajen rayuwar yau da kullum, daga daukar ruwa zuwa daukar kaya da kwashe amfanin gona.

Wannan ya sa wasu kasashe yin dokar hana cinikin fatar, cikin su harda Botswana da Senegal da Mali da Burkina Faso da Gambia, yayin da Zimbabwe ta rufe wani gida da ake amfani da shi wajen yanka jakunan ana sayar fatun su kamar yadda Habasha tayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.