Isa ga babban shafi
Madagascar

An fara shari'ar wadanda ake zargi da yunkurin juyin mulki a Madagascar

Gwamnatin Madagascar ta ce yau za’a fara   mutane 21 shari’a dangane da tuhumar da ake musu na hannu wajen yunkurin juyin mulki, cikin su   wasu ‘yan kasar Faransa  biyu da matansu.

Shugaban Madagascar Andriy Rajoelina.
Shugaban Madagascar Andriy Rajoelina. AFP/File
Talla

An dai kama Paul Rafanoharana da Philippe Francois tare da matan su ne a ranar 20 ga watan Yuli saboda zargin cin amanar kasa da hada baki da kuma yunkurin kashe shugaban kasa Andry Rajoelina.

Babban mai gabatar da kara na zargin mutanen 21 da kaddamar da wani shirin hallaka fitattun mutanen kasar cikin su harda da shugaban kasa.

Mutanen dai sun ki sun musanta laifukan da ake zarginsu da aikatawa tuhumar.

Babu wani karin haske a kan ko za a bari ‚yan jarida su halarci shari’ar, wadanda lauyoyin da ke kare wadanda ake zargin suka ce za a shafe kwanaki 3 ko 4 ana yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.