Isa ga babban shafi

Kotu ta daure tsohuwar daliba saboda almubazzarancin dala miliyan 1

Wata kotu a kasar Afirka ta kudu ta daure wata tsohuwar dalibar jami’a shekaru 3 a gidan yari, saboda yadda ta dinga facaka da kudin da ya kai Dala miliyan guda da aka tura mata a asusun jiyar bankin ta cikin kuskure.

Dalar Amurka
Dalar Amurka REUTERS - JOSE LUIS GONZALEZ
Talla

Dalibar Sibongile Mani mai shekaru 31 na saran samun Dala 100 a matsayin kudin tallafin karatu, amma sai aka tura mata Dala miliyan guda cikin kuskure.

Maimakon da Mani ta mayar da kudin, sai kawai ta kama sayayya iri iri ciki harda kayan sawa da wayar salula da kuma zuwa taron rawa inda ta kashe Dala 56,000, bayan  kwashe watanni biyu tana kashe kudin har zuwa lokacin da aka fahimci inda kuskuren yake.

Wasu mutane na kallon daurin shekaru 3 a matsayin wanda yayi tsanani a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.