Isa ga babban shafi
Afirka ta Kudu

Kusan mutum 400 ambaliyar ruwa ta kashe a Afirka ta Kudu

Shugaban Kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi kira da a yi addu'o'i ga mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa da su yayin wani jawabin bukukuwar Easter a wata Mujami’a, dai-dai lokacin da adadin wadanda suka mutu sakamakon bala'in ya kai kusan 400.

Wasu gidaje da Ambaliyar ruwa ta lalata a Ntuzuma, a wajen Durban, Afirka ta Kudu, 12 ga watan Afrilu, 2022.
Wasu gidaje da Ambaliyar ruwa ta lalata a Ntuzuma, a wajen Durban, Afirka ta Kudu, 12 ga watan Afrilu, 2022. AP - STR
Talla

Kwanaki biyar bayan da iftila’in Ambaliyar ya auku  a kudu maso gabashin birnin Durban da ke gabar tekun da kewayensa, har yanzu ba’a kai ga gano mutane da dama da suka bace ba, yayin da masu aikin ceto suka fadada aikinsu, cikin harda 'Yan sanda da sojoji.

Shugaban kasar Afirka da Kudu Cyril Ramaphosa wanda ke jawabi kan bukukuwan Easter a mujami’ar El-Shaddi dake gabashin birnin Ermelo, ya bukaci yin addu’i ga daruruwan mutane da suka rasa rayukansu, da kuma wadanda suka jikkata a yankin na KwaZulu-Natal.

Ramaphosa ya ce ya ziyarci dangin da suka rasa mutane 10 ciki har da kananan yara sakamakon Ambaliyar da ya kira bala’i da kasar bata daba gani ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.