Isa ga babban shafi

Ana tuhumar Ramaphosa da sakaci wajen kare rayukan 'yan Afirka ta Kudu

Gamayyar kungiyoyin masu fafutukar yaki da matsalar sauyin yanayi sun garzaya kotu inda suka yi shigar da kara kan shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da wasu fitattun ministocinsa, bisa zarginsu da yin sakacin rashin daukar kwararan matakan magance matsalar ta sauyin yanayi a wasu sassan kasar.

Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa yayin jajantawa mutanen da ambaliyar ruwa da kuma guguwa suka tagayyara a yankin KwaZulu Natal.
Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa yayin jajantawa mutanen da ambaliyar ruwa da kuma guguwa suka tagayyara a yankin KwaZulu Natal. AP - Kopano Tlape
Talla

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da alkaluman jami’an agaji suka tabbatar da mutuwar mutane kusan 400 a lardin KwaZulu Natal, inda guguwar Issa ta tafka barna, inda baya ga hasarar rayukan da ya sanadi, guguwar ta lalata gine-gine da manyan tituna da ababen more rayuwa amsu yawan gaske.

Masu rajin yaki da matalar sauyin yanayin da ke karkashin gamayyar kungiyar CJCM, sun tuhumi gwamnatin Cyril Ramaphosa da zama sanadin mutuwar dimbin mutane sakamakon kin daukar matakan kare muhalli da suka hada da rage yawan gurbatacciyar Iska, da kare mutane masu rauni.

Karin laifin da masu fafutukar ke zargin shugaba Cyril Ramaphosa da aikatawa kuma shi ne nuna halin ko in kula da karuwar matsalar rashin daidaito da kuma talauci, a yankunan da ke gabar ruwa, musamman ma yankin KwaZulu Natal da ya sha fama da guguwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.