Isa ga babban shafi
Afirka ta Kudu - Ambaliya

Ambaliyar ruwa a Afirka ta Kudu ta yi sanadin mutuwar sama da mutum 400

Adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afka wa gabar tekun gabashin Afirka ta Kudu ya kai sama da 400, ciki har da mai aikin ceto, kamar yadda wani jami'in yankin ya baiyana, yayin da wasu da dama suka bace.

Ambaliayar ruwa ya lalata Gidajen mutane a Ntuzuma, dakr wajen Durban, na  Afirka ta Kudu, ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, 2022.
Ambaliayar ruwa ya lalata Gidajen mutane a Ntuzuma, dakr wajen Durban, na Afirka ta Kudu, ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, 2022. AP - STR
Talla

Adadin wadanda suka mutu a halin yanzu ya kai sama da 400, a cewar Sihle Zikalala, firaministan lardin KwaZulu-Natal yayin da yake zanta wa da manema labarai, inda ya kara da cewa wasu mutane 63 har yanzu ba a gano inda suke ba.

Wasu da suka tsira daga Ambaliayar ruwa Afirka ta Kudu, na neman ruwan sha, Talata, 12 ga watan Afrilu, 2022.
Wasu da suka tsira daga Ambaliayar ruwa Afirka ta Kudu, na neman ruwan sha, Talata, 12 ga watan Afrilu, 2022. AFP - RAJESH JANTILAL

Daya daga cikin masu aikin lalubo wadanda wannan iftila’in ya rutsa da su ya fuskanci matsalar sarkewar numfanshi wadda sai daukar shi a aka yi cikin gaggawa zuwa asibiti sa’adda daga bisani yace ga garin ku.

Ruwan sama ya fara barkewa a yankin gabashin afirka ta kudun ne da ambaliyar ruwa ya yi kamari, lamarin da ya ba da damar gudanar da bincike da ayyukan agaji bayan da wata guguwa mafi muni da da baza a mace da da’ita ba ta faru a yankin.

wasu daga cikin mutanen da ambaliya ta ritsa da su a Afrika ta kudu
wasu daga cikin mutanen da ambaliya ta ritsa da su a Afrika ta kudu AP - Kopano Tlape

Ambaliyar ruwa ta mamaye wasu sassan birnin Durban ne da ke gabar tekun kudu maso gabashin kasar a farkon makon da ya gabata tare da kashe hanyoyi, da lalata asibitoci da kuma share gidaje da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.