Isa ga babban shafi

Shugaba Cyril Ramaphosa ya shelanta cewa kasar sa na cikin halin iftila’I

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta tura dakaru 10,000 don taimakawa wajen dawo da wutar lantarki da ruwan sha tare da neman mutane 63 da suka bace bayan wata kakkarfar guguwa da ta haifar da ambaliyar ruwa mafi munin gaske a Afrika ta kudu.

Shugaban Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa
Shugaban Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa AFP - EMMANUEL CROSET
Talla

Mako guda bayan ruwan sama da ba a taba ganin irinsa ba a birnin Durban da lardin KwaZulu-Natal, wanda ya yi sanadiyyar rayukan mutum 443.

Rahotanni daga kasar sun ce, ruwan sun lalata tituna da dama, haka zalika akwai yankunan da aka gaza kai musu dauki saboda lalacewar hanya.

wasu daga cikin unguwanin da ruwa suka afkawa a Durban na Afrika ta Kudu.
wasu daga cikin unguwanin da ruwa suka afkawa a Durban na Afrika ta Kudu. AP - STR

Guguwa mafi muni da aka yi a tarihin kasar, ta haifar da ruwan sama mai karfi a Durban da kewaye.

Kimanin mutane 40,000 ne suka rasa matsuguni sannan sama da makarantu 550 da cibiyoyin kiwon lafiya kusan 60 suka lalace.

A yau talata nan ne ake sa ran yara da dama za su koma aji bayan hutun bikin Easter, amma hukumomi sun yi gargadin cewa dalibai 271,000 ba za su iya komawa ba saboda lalacewar makarantu.

Wasu da suka tsira daga Ambaliayar ruwa Afirka ta Kudu, na neman ruwan sha, Talata, 12 ga watan Afrilu, 2022.
Wasu da suka tsira daga Ambaliayar ruwa Afirka ta Kudu, na neman ruwan sha, Talata, 12 ga watan Afrilu, 2022. AFP - RAJESH JANTILAL

Gwamnati ta bada sanarwar bayar da agajin gaggawa na rand biliyan daya kwatankwacin dalar Amurka miliyan 68.

Har yanzu dai kasar na fafutukar ganin ta murmure daga annobar cutar sarkewar numfashi ta Covid da kuma tarzomar da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 350, a shekarar bara, ‘uwa ‘uba kuma yanzu ambaliyar ruwan da ta haifar da asarara dukiyoyi da rayuka, galibi a yankin kudu maso gabashin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.