Isa ga babban shafi

Wani tsohon jami'in yan sanda, da ya taka rawa a kisan kiyashin kasar Rwanda, ya shiga hannu

Jami’an binciken  Majalisar Dinkin Duniya sun baiyana nasarar da aka cimma ta damke daya daga cikin mutane 4 da ake nema ruwa jallo, Fulgence Kayishema, bisa laifin kitsa kisan kiyashin da aka aikata a 1994 a kasar Rwanda. An dai yi sa’ar kama shi ne a kasar Afirka ta kudu, a yayin da ake cigaba da fafutukar nemansa, tare da sauran abokan tafiyar sa. 

kwarangwal na kasusuwan mutanen da aka yi wa kisan kiyashi a Rwanda
kwarangwal na kasusuwan mutanen da aka yi wa kisan kiyashi a Rwanda AP - Ben Curtis
Talla

A ranar laraba da ta gabata ne aka samu nasarar kama Fulgence Kayishema, daya daga cikin wadanda ake nema ruwa a jallo a duniya a Parl na kasar Afirka ta Kudu, sakamkon wani aikin bincike na hadin gwiwa da aka gudanar. 

A wancan lokacin anyi wa akalla mutane dubu dari 8 musaman  ‘yan kabilar Tutsi kisan kiyashi ta hanyar yi yankan rago, bayan da suka shafe sama da kwanaki  100 a hannun ‘Yan kabilar Hutu. 

Yanzu haka dai Kayishema, da ya kasance tsohon Sifeton ‘Yansanda, na fuskantar tuhume tuhume da dama, da suka hada da aikata kisan kiyashi, cin zarafi bil’adam kuma hadin baki wajen gallazawa al’uma. 

Ana zargin tsohon Sifeton ne da aikata laifin kisan ‘yan kabilar Tutsi sama da 2000, wadanda ke zaman neman mafaka a wata majami’ar katolika dake Kituru a shiyar Kivumu. 

An kuma same shi da hanu, wajen shirya kisan kiyashin da kuma sayen man fetur din da aka yi amfani da shi wajen kone wata majami’a dake kunshe masu neman mafaka yan kabilar Tutshi   a ciki. 

A cewar hukumar binciken masu aikata laifuka ta MICT Kayishema, mai shekaru 60 da haihuwa ya tsere ne tun a watan yulin shekarar 2001 kafin ya shiga hanu a wannan  mako,  domin fuskantar tuhumar munanan aiyukan da aka samu hanun sa a ciki.   

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.