Isa ga babban shafi

Togo ta ba da damar amfani da tashoshin jiragen ruwanta don kai agaji Nijar

Gwamanatin Togo ta amince Majalisar Dinkin Duniya ta yi amfani da tashoshin jiragen ruwanta domin isar da kayayyakin agaji ga al’ummar jamhuriyar Nijar, bayan da Majalisar ta nemi wannan alfarma daga mahukuntan kasar ta Togo. 

Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbé.
Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbé. © Gnassingbe Twitter
Talla

 

A cikin kwanakin da suka gabata ne Mataimakin babban magatakardar na Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ayyukan jinkai ya gabatar wa Kungiyar Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO da bukatar sassauta takunkuman da aka sanya wa Nijar biyo bayan juyin mulki da sojoji suka yi, wanda hakan zai bayar da damar isar da kayan agaji wa jama’a. 

Takunkumi na cutar da Nijar

A wasikarsa zuwa ga Ecowas, jami’in na Majalisar Dinkin Duniya ya ce takunkuman da kungiyar ta sanya wa Nijar na matukar cutar da jama’a marasa karfi ne, saboda haka bai kamata matakan da kasashe ke dauka, biyo bayan kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum su hana gudanar da agaji ga mabukatansa ba. 

Biyo bayan wannan korafi na Majalisa Dinkin Duniya ne, kungiyar ta ECOWAS ta tunkari kasashe mambobinta domin jin ra’ayoyinsu, bayan an tuntube ta, gwamnatin Togo ta bakin ministanta na harkokin waje Robert Dussey, ta bayyana wa shugaban kungiyar Omar Alieu Touray cewa ta amince kayayyakin da za a tura Nijar su ratsa kasar. 

Saura Benin

Ko baya ga Togo, kungiyar ta Yammacin Afirka ta rubuta makamanciyar wannan wasika ga Jamhuriyar Benin, domin ita ma ta bayar da damar yin amfani da tashoshin ruwanta da kuma iyakokinta domin isar da kayan jinkai a Nijar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.