Isa ga babban shafi

Mali ta aike da dakarunta da sojojin hayar Wagner zuwa arewacin kasar

Dakarun Mali da sojojin hayar kamfanin Wagner na Rasha, sun isa garin Tessalit da ke arewacin kasar, inda nan ba da dadewa ba dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya za su fice.

Wani sojan rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kusa da garin Menaka da ke kasar Mali.
Wani sojan rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kusa da garin Menaka da ke kasar Mali. © Florent Vergnes, AFP
Talla

Wani jami'in soji a arewacin Mali ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, tun a ranar Alhamis sojojin suka isa garin na Tessalit.

Bayanai sun ce tun cikin watan Agusta rundunar MINUSMA ta mika wasu sansanoninta ga sojojin Mali, gabanin ficewarta daga kasar a karshen wannan shekara ta 2023.

Matakin dai wani bangare ne na sake fasalin tsaron Mali da gwamnatin sojin kasar ta fara, tun bayan da ta kwace mulki a shekarar 2020.

A baya-bayan nan dai mayakan 'yan awaren Abzinawa, da suka yi sulhu da gwamnati a shekarar 2015, sun sake daukar makamai, yayin da kungiyar GSIM mai alaka da Al-Qaeda ta zafafa kai hare-hare kan sojojin Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.