Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta mamaye yankuna 38 na kasar Kenya

Gwamnatin kasar Kenya ta bukaci mazauna yankunan da ambaliyar  ruwa ya yiwa barna, da kauce daga wuraren, yayin da ake hasashen ruwan sama mai karfin gaske na tunkarar kasar da ke yankin Gabashin Afirka.

Wuraren da wannan ambaliya tafi yiwa barna sun hada da birnin Mombasa da kuma Malindi, hadi da yankunan da ke arewacin kasar masu iyaka da Somalia.
Wuraren da wannan ambaliya tafi yiwa barna sun hada da birnin Mombasa da kuma Malindi, hadi da yankunan da ke arewacin kasar masu iyaka da Somalia. © TheWeather
Talla

Akalla mutum 76 hukumomin kasar suka tabbatar sun rasa rayukansu, inda sama da 40,000 suka rasa muhallansu tun daga lokacin da ruwan ya fara sauka a watan Oktoba.

Tuni shugaban kasar, William Ruto, ya kira taron gaggawa bayan da hukumomi suka tabbatar da cewa daga cikin yankuna 47, ambaliyar ruwan ta shafi yankuna 38 daga cikinsu.

Mai Magana da yawun gwamnatin kasar, Hussein Muhammad, ya lura da cewa an samu rahoton barkewar cutuka masu yaduwa da kuma lalacewar gine-gine a yankuna da dama na kasar ta Kenya.

Wuraren da wannan ambaliya tafi yiwa barna sun hada da birnin Mombasa da kuma Malindi, hadi da yankunan da ke arewacin kasar masu iyaka da Somalia.

A garin Garissa, hukumomi sun ce dubban mutane ne suka rasa gidajen su, inda ruwan ya mamaye gadoji da kuma manyan hanyoyi, abin da ya haifar da matsala wajen isar da kayan agaji ga yankuna da dama.

A kasar Somalia, mutum 96 ne suka rasa rayukansu sakamakon mummunar ambaliyar ruwan, inda 44 suka mutu a kasar Habasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.