An kammala shara’ar aikata laifin kisan kiyashin ga wasu yan kasar Rwanda biyu a Belgium
Wallafawa ranar:
An kawo karshen shara’ar kisan kiyashin da ake yi wa wasu yan kasar Rwanda biyu a kotun Bruxelles na kasar Belgium.
A cikin daren ranakun alhamis zuwa safiyar juma’a ne, kotun ta yanke wa Séraphin Twahirwa, dan shekaru 66 hukumcin daurin rai da rai. Tare da bada umarnin daure Pierre Basabose, mai shekaru 76 a duniya, duk da cewa, ya na fama da matsalar tabin hankali, da kuma tsufa kamar yadda likitoci suka sanar.
A ranar talatar da ta gabata ne, kotun ta bayyana mutanen biyu a matsayin wadanda suka aikata laifin kisan kiyashi da laifukan yakin da aka aikata a tsakanin watan avrilu zuwa yunin 1994 a kasar Rwanda
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu