Isa ga babban shafi

Jam'iya mai mulki a Afirka ta kudu ANC ta kaddamar da yakin neman zabe

Jam'iyar ANC mai mulki a kasar Afirka ta Kudu ta kaddamar da yakin neman zabe duk kuwa da irin sukar da ta ke samu daga al'umar kasar.

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa.
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa. AP - Themba Hadebe
Talla

Jam’iya mai Mulki a Afirka ta kudu ANC ta kaddamar da yakin neman zabenta ne a ranar asabar dinnan tare da shirin kawo ga karshen tashin hankali da a ciki a kasar na rashin wadatattacen aikin yi tare da magance matsalar tafiyar kaguwar da tattalin arzikin kasar ke fuskanta.

Tun dai kafuwar mulkin dimokaradiya a shekarar 1994 jam’iyar ANC ke shan suka, musamman akan cin hanci da rashawa da kuma rashin iya tafiyar da lamura yadda ya kamata.

Sai dai duk da sukar, jam’iyar ta ANC  itace kan gaba wajen magoya baya daga dukkanin matakai a fadin kasar musamman sakamakon namijin kokari da ta yi wajen yakar mulkin wariyar launin fata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.